Monday, 23 April 2018

DOMIN DAIDAITA AL'ADAR MACE

Mace tun tana shekara 13 ko 14 take zama daya daga cikin masu jinin al ada har zuwa shekara 50 to daga nan malamai sun tabbatar hukunci jinin haila ya sauka akanta koda tanayi


,

kowacce mace da lokacin yin al'adarta amma mafi yawan mata sunayi afarkon wata kuma yanda ya saba zuwa idan ya canja ya zama na cuta kuma ya zama babu hukunci akansa 


wani lokacin jini yana daukewa mace amma bayan ta sadu da mijinta sai taga jinin ya dawo to irin wannan ya kamata mace tarinka amfanida auduga ko farin kyalle wajen ganewa ko akwai saura domin akwai macenda koda ya dauke ba aso tayi gaggawar saduwa da mijinta anaso A kalla asamu sa'o,i ashirin da hudu (24hours) sannan tayi wanka,lokacinda mace tasamu ciki shi wannan jinin yana daukewa ya zama abincin wannan jaririn shiyasa idan mace tanada ciki bata ganin jini saidai idan na cutane shima wannan bashida hukuncin jinin al'ada saidai duk lokacinda mace zatayi sallah saita sake alwala


wa, CIWON MARA 

Mata musamman wadanda basuda aure suna ciwon mara irin wannan kuma dattin maniyi ne domin ita mace maniyinta yana kasan nononta lokacinda sha awa tayi mata yawa zai dawo mararta idan be fitaba lokacin al ada saiya dinga mata ciwo 

RIKICEWAR AL'ADA

Koda yake ana samun canjawar lokacin zuwan al'ada kwanaki uku zuwa biyar to amma rikicewar sa alamune na matsala kuma ciwon sanyi (infection) shine kan gaba wajen kawo matsalar rikicewar al'adar mace,

Ana samun matsalar aljanu suma sukan jawo matsalar rikicewar al'ada don haka me fama da wannan matsala ta nemi magani.

WASU DAGA CIKIN MAGUNGUNAN

Ga wadanda ciwon sanyi ya jawo musu matsalar sai a samu habbatussauda cokali 3 sai garin kustul hindi cokali7garin shazabu cokali3 sai asamu zuma kofi biyu azubasu agauraya ana shansa safe da yamma saikuma a samu garin albanuna ana zuba cokali daya acikin ruwa kina wanka dashi su kuwa wadanda suke fama da matsalar aljanu saisu garzaya wajen masu rukiya sannan a samu Garin Kustul Hindi kamar cokali guda Garin Hulba ma haka. Ki rika tafasawa kina sha In sha Allahu al'ada zata daidai tu

Sannan 'Ya'yan Habbatus sauda idan ana taunawa ana hadiyewa in sha Allahu za'a samu lafiya

Tuesday, 10 April 2018

YANDA AKE GYARA NONO KOWANNE IRI

 

GYARAN NONO

mace tana fara fitar da nono daidai lokacin fara jinin al'ada yayinda allah ya banbanta halittar sa jinsi daban daban ta yanda jinsin al'ummar africa bakaken fata ya banbanta dana wasu kasashen don haka abu na farko daya kamata jama'a su fara sani akwai banbanci tsakanin nonon baturiya dana bakar fata  dan haka maganin gyaransu da namu ya banbanta

dan haka idan gyara nono kikeso girmansu ko tsayuwarsu tareda kyawunsu ba tareda yayi miki illah ba dole saidai kiyi amfanida na gargajiya.

akwai banbanci tsakanin tsayar da nono da girmansa to amma saidai abu daya baya samuwa dole sai an hada da wani ma'ana bazaiyu nono ya tsaya kadai ba har sai girmansa ya karu haka zalika bazaiyu ace nono ya girma ace bai tsayaba kuma wadanda sukafi matsala a gyara nono sune wadanda ya kwanta  shiyasa duk maganinda zai kara girman nono kuma ya tsayar dashi zai zama na musamman sannan za'a dauki lokaci ana  shansa sabanin wanda kawai cikowa take bukata.

nonon mace yanada suffa kala kala nayi kokarin binciko bayanai akayi dareda bin diddigin magunguna daya dace masu suffar nonon suyi kai harma wanda zaiyi da kowanne1 na farko AKwai nono mai (mango Shape) wato Shine wanda bakinsa (nipples) yaKe Kallon sama irin wannan nonon baya zubewa da wuri irn wannan batashan wahalar gyara dan haka

zaki iya wannan yanda zakiyi ki samu ayaba (plantain) ki yanyankata ta bushe sannan ki daka garin to saiki samu aya ki  wanketa kisaka gyada kisaka amarkada miki

saiki tace ruwan kina diban wannan garin plantain din kina zuba madara peak kinasha kamar sau biyu arana kafin sati daya zakiga canji sosai nononki zasu tashi su ciko.


? sai kuma me bi masa wato (Pointed breast) shine zakuga yana kallon gaba (straight) gasKiya irin wannan nonon yana saurin faduwa domin riga kafin faduwarsa arinka kunun alkama wato  idan aka nika alkamar sai ayi kununta asaka nono da zuma anasha, idan kuma zubewa yayi


zaki hada farar shinkafa da alkama da garin habatussauda da aya da gyada ki nikasu suyi laushi ki tankade sai ki ajiye wannan garin kina hadashi da nono kinasha kullum wannan shine hadinda  zaisa nono ya ciko ya kara girma kuma ko budurwa zata iyayi..


?Akwai nono mai Kallon gefe (left and right) zakuga aKwai nisa sosai a tsaKanin nonuwa biyun zai iya kallon hagu ko dama wadannan sune sukafi matsala domin sa'ar mace wannan nono su zama kanana amma da zaran sun dan fara tashi to tabbas ta rasa nono domin gyaransu su dawo dole sai kinyi amfanida maganin nonon na musamman wato gari da akesha na kwana 30 ko 25 wannan kowanne irin nono mace take dashi zai  temaka mata


Domin anyi amfanida ingantattun magunguna kuma na gargajiya, gadalin nono da nonon kurciya da 'ya'yan  baure kumbura fage zakiyi garinsu

idan suka bushe a inuwa saiki samu hulba me kyau ki hada sai kuma kisamu aya da  alkama da ridi da gyada da fafar shinkafa da waken suya

  

dukkansu ki gyarasu kamar gyada da ridi da waken suya saiki  soya su sai kiyi garinsu adakasu ko nikawa saiki samu ruwan zafi  kamar rabin kofi ki zuba garin cokali daya ki gauraya ki zuba zuma ko zugar da nono ko madara ta ruwa peak kinasha kullum kafin wani lokaci zasu tashi koda kanana ne

Create by Auwal Azare 08133484236

Tuesday, 13 February 2018

MEYE AMFANIN ALBASA?

1-- Albasa tana tacewa jinin jikin 'Dan Adam. Duk mutumin da yake fama da matsalar karancin jini, ya yawaita cin
albasa. insha Allahu jininsa zai
yawaita.

2--
Wanda yake fama da ciwon SICKLE
(CELL ANEMIA) ya rika yanka albasa tare da Ganyen Zogale yana ci. Insha Allahu wannan ciwon Sickler din zai
yi sauki

3--Wanda yake shan wahala wajen yin fitsari ko
 bahaya, ya nemi Man albasa ya
gauraya da zuma da lemon tsami. ya
rika sha safe da yamma. kuma ya rika shafa man albasa ajikin Mararsa shima insha Allahu zai samu waraka cikin
lokaci kankani.

4--sai kuma ciwon sugar Duk mai fama da yawan fitar fitsari saboda diabetes
(Ciwon Sugar) ya nemi albasa mai kyau ya rika yankawa kullum yana ci.Insha Allah sugansa zai sauka, kuma zai dena yawan fita fitsarin

5--mata masu zubewar gashi duk matar da
take fama da zubar gashi ko
kwarkwata ko amosani ta samu
 man albasa da Man ridi da kuma garin Baqadunas ta kwaba ta rika shafawa a matsirar gashinta kullum kafin ta
kwanta barci da safe sai ta
wanke da ruwan zafi ta ci gaba da yin haka har tsawon kwana bakwai

6--daga karshe me ciwon basir ana yanyanka albasa a dafata sannan ayi kwadonta da kuli (karago) arinka ci kullum insha allahu za ayi mamaki


LURA DA WANNAN RUWAN AGABAN MACEkamar yanda kowa yasani gaban mace baya rabuwa da jika ko na ni ima ko kuma na cuta ya danganta da irin ruwan

idan akace farin ruwa ana nufin fari kal me kamar ruwan famfo shine yake zama na ni ima kuma yanada yauki sannan yanada dandano wani kamar gishiri ya danganta da irin abunda mace kesha

saidai mata da yawa farkon saduwa akwai wani farin ruwa me kamar nono dan kadan yana fitowa wannan wani ruwane wanda ba kowacce mace ke samuba domin da yawa mace daga ta fara haifuwa shikenan kuma wannan ruwane na musamman farar mace

wani ruwan kuma yauki zakaga yanayi kuma haka kawai mace ko zance tayi da namiji zataganshi kuma me irin wannan ruwan bata taba bushewar gaba kuma daban take acikin mata

shikuma ruwa na cuta haka kawai yake zuwa agaban mace kuma bayan farine me kamar majina zakaganshi guda guda wani kuma kamar zare zare kuma ruwan yana iya canja kala daban daban wani yakoma Green wani brown kuma sauda dama warinsa yana zama kamar na danye kifi akwai kuma me warin danyen kwai

wani ruwan kuma kamar mace me ciki tana yawan ganinsa musamman bayan gama saduwa ko kuma bayan ta gama fitsari wannan shikuma dattine na mahaifa shima ba matsala bane

dalilai da yawa suna saka mata kamuwa da ciwon sanyi saboda idan namiji yanada dashi zai iya sakawa mace ga kuma shiga kowanne toilet ko wajen tsugo a toilet sannan kuma koda mata hudune agida aka samu daya me wannan cutar tana iya sakawa sauran shiyasa mata masu hikima basa rabuwa da riga kafin cutar wato kamar sabulai da ruwan magarya da amfanida gishiri da sauransu


ZUMAR NAMIJI

maza kadai ke shanta shiyasa kirarinta zumar namiji wanda kuma wannan zuma aikinta ajikin namiji shine hanashi saurin inzali (rilessing) me yuwa kayi mamaki idan kasha wannan zumar amma kaji wani dandano kamar bana zuma ba to bari kaji yanda akeyinta nan zakasan dole dandanonta ya canja amma kafinnan yanada muhimmanci kasani ba'a shanta sai sa'o.i uku kafin a kwanta da mace wato jima.i kuma cokali babba guda hudu sun isheka sannan kuma anaso asha bayan anci abinci
sassaken kalgo tareda 'ya'yansa ake hadawa da sauyar gaude da hulba sai ayi garinsu azuba acikin wannan zuma tacecciya farar saka sai amatsa lemon tsami aciki agauraya sosai yanda zai hade


GWARZON NAMIJI

littafin gyaran gida na PDF http://k003.kiwi6.com/hotlink/d04m4e6xsn/GWARZON_NAMIJI_.1_and_2.pdf littafin gyaran gida na APK h...