Tuesday, 21 February 2017

AMFANIN HULBA WAJEN GUARAN JIKI

1 . Zaki samu garin hulba ki dama da madara

da zuma ya damu sosai sai ki shafa a fuskarki ki

barshi yayi kamar minti talatin (30minutes) kafin kiyi wanka

lokacinda kikazo wanka saiki wanke wannan zaisa fuskarki tayi kyau tayi sheki kuma zai kashe miki kananan kuraje (pimples)


GYARA GASHI,


ki hada man hulba da man kwakwa ki gaurayashi sosai sannan ki shafa akanki yayi sa a daya (1hour) saiki wanke kuma zakiyi sau biyu a mako daya (1wek) har zuwa mako uku (3weks) gashinki zai kara kyau na yayi tsawo yayi baki ga sheki


GIRMAN NONO

idan kika hada garin hulba da nono ko madara kika dafasu suka zama kamar kunu kinasha zaisa nononki yayi girma kuma zai temakawa me shayarwa wajen samun ishashen ruwan nono ta yanda koda kin gama shayarwa nononki bazai kankanceba..


barkanmu da ibada ina fatan zamusha ruwa lafiya...

No comments:

Post a Comment

                                      DAREN AMARCI 1&2 DOWNLOAD