idan ciwon basir ya hanaka gamsarda iyalinka wato ya kashe maka jijiyoyin azzakari basuda karfi ka jarraba hada wannan maganin
Wato anemi sassaken dinya da saiwar tsada da saiwar sabara
Amma yakamata sassaken dinyar yafi yawa sosai dukkansu a dakasu sai a gauraya.
Kullum arinka dibar cokali daya a dafa da ruwa kofi daya sannan a tache asha har zuwa mako daya (1week)
idan kuma basir din yana tsirowa to Sassaken dinyar za a samu a dafashi tun yana danyensa Sannan a surka ruwan daidai misalin yadda baza a chutu dashi ba.
Sannan a juye acikin bahon
wankanka, sai a rinka zama aciki
to a bangaren maganin islamic kuma asamu Garin Habbatus Sauda kamar cokali 3 sai a hada da Garin sassaken Dinyar shi kuma cokali 1 a saka garin citta cokali.1 sai a samu zuma kamar copy karami ka zuba ka gauraya karin a shan cokali2 safe da rana da yamma wato sau uku a rana
idan tsirowa basir din yakeyi za a iya samun garin Hulba da bagaruwa da kuma garin sassaken dinya ka rinka dafawa ana zama acikin ruwan zafin
wadannan magungunan dukkansu sun inganta domin mun dade da jarrabasu
No comments:
Post a Comment