(1) Ki surfa sannan ki wanke gero ki baza shi ya bushe ki samu farar shinkafa ki dan soyata ki hada su ki dakasu. Ki bare bawon kankana da kwallayenta da kuma bawon cucumber ki hada su su bushe ki dake su da geron ki dinga sha da peak ko nono
(2) shi kuma Wannan geron kuma bayan kin surfashi ki baza shi ya bushe ki saka kanumfari da mazarkwaila da geron mata da minannas ki dakasu ki dinga sha da madarar shanu ko madara peak
(3) kawai ki surfa gero ki zuba ruwa sannan ki dora shi a wuta ki zuba kanumfari da danyan manshanu kiyita bashi wuta har geron yayi laushi sai ki tace wanna ruwan shine zaki wuni kinasha da duminsa
No comments:
Post a Comment