Monday 23 April 2018

DOMIN DAIDAITA AL'ADAR MACE

Mace tun tana shekara 13 ko 14 take zama daya daga cikin masu jinin al ada har zuwa shekara 50 to daga nan malamai sun tabbatar hukunci jinin haila ya sauka akanta koda tanayi


,

kowacce mace da lokacin yin al'adarta amma mafi yawan mata sunayi afarkon wata kuma yanda ya saba zuwa idan ya canja ya zama na cuta kuma ya zama babu hukunci akansa 


wani lokacin jini yana daukewa mace amma bayan ta sadu da mijinta sai taga jinin ya dawo to irin wannan ya kamata mace tarinka amfanida auduga ko farin kyalle wajen ganewa ko akwai saura domin akwai macenda koda ya dauke ba aso tayi gaggawar saduwa da mijinta anaso A kalla asamu sa'o,i ashirin da hudu (24hours) sannan tayi wanka,



lokacinda mace tasamu ciki shi wannan jinin yana daukewa ya zama abincin wannan jaririn shiyasa idan mace tanada ciki bata ganin jini saidai idan na cutane shima wannan bashida hukuncin jinin al'ada saidai duk lokacinda mace zatayi sallah saita sake alwala


wa, CIWON MARA 

Mata musamman wadanda basuda aure suna ciwon mara irin wannan kuma dattin maniyi ne domin ita mace maniyinta yana kasan nononta lokacinda sha awa tayi mata yawa zai dawo mararta idan be fitaba lokacin al ada saiya dinga mata ciwo 

RIKICEWAR AL'ADA

Koda yake ana samun canjawar lokacin zuwan al'ada kwanaki uku zuwa biyar to amma rikicewar sa alamune na matsala kuma ciwon sanyi (infection) shine kan gaba wajen kawo matsalar rikicewar al'adar mace,

Ana samun matsalar aljanu suma sukan jawo matsalar rikicewar al'ada don haka me fama da wannan matsala ta nemi magani.

WASU DAGA CIKIN MAGUNGUNAN

Ga wadanda ciwon sanyi ya jawo musu matsalar sai a samu habbatussauda cokali 3 sai garin kustul hindi cokali7garin shazabu cokali3 sai asamu zuma kofi biyu azubasu agauraya ana shansa safe da yamma saikuma a samu garin albanuna ana zuba cokali daya acikin ruwa kina wanka dashi 



su kuwa wadanda suke fama da matsalar aljanu saisu garzaya wajen masu rukiya sannan a samu Garin Kustul Hindi kamar cokali guda Garin Hulba ma haka. Ki rika tafasawa kina sha In sha Allahu al'ada zata daidai tu

Sannan 'Ya'yan Habbatus sauda idan ana taunawa ana hadiyewa in sha Allahu za'a samu lafiya

                                      DAREN AMARCI 1&2 DOWNLOAD